Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina Ta Karrama Wani Consitabil Da Ya Tsinci Makudan Daloli Kuma Ya Mayar Ga Mai Su

Alfijr

Alfijr ta rawaito rundunar ƴan sandan ta karrama wani dan sanda Consitabil Nura Mande, wanda ya tsinci kudin kasar waje dala 800 ya kuma mayar dasu ga mai shi a jihar Katsina ranar Juma a

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, ya fitar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Idris Dabban, ya mika wa dan sandan takardar yabo da kuma N30,000 don girmama shi kan irin kyakkyawan hali da ya nuna.

Alfijr

Mande yana bakin aiki a sansanin jin dadin alhazai na jihar Katsina inda ya gano dala 800 na wata mata mai niyyar aikin hajji mai suna Hajiya Hadiza Usman.

Salisu-Rumah ya yaba wa dan sandan bisa kyawawan halayensa da rikon amana.

A cewar Isah, kwamishinan ‘yan sandan ya ji dadin yadda Maude ya nuna gaskiya, ya kuma yi kira ga sauran ‘yan sandan da ke cikin rundunar da su yi koyi da shi.

Alfijr

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaba wa jami’anta wadanda suka nuna gaskiya da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

Kamar yadda NAN ta wallafa

Slide Up
x