Daga Aisha Salisu Ishaq
Sabon Shugaban Hukumar Filayen Jiragen Sama ta kasa FAAN Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya kai ziyarar sa ta farko ga hukumar ta FAAN a yau, 18 ga Fabrairu, 2024.
Alfijir labarai ta rawaito babbar daraktar hukumar ta FAAN, Olubunmi Kuku, ta gabatar da cikakken bayani ga shugaban kan ayyukan hukumar. A cikin jawabinta, ta gabatar da rahoton nasarorin da aka samu da kuma kalubalen da hukumar ta fuskanta cikin shekarar da ta gabata.
Daga bisani, tawagar shugabannin FAAN karkashin jagorancin Babbar Darakta ta jagoranci shugaban da tawagarsa wajen rangadin wasu muhimman wurare a Filin Jirgin Saman Murtala Muhammed da ke jihar Legas, domin tantance yanayin kayayyakin aiki a filin jirgin.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ