Ɗan takarar gwamnan Kano na jamiyyar APC da kotu ta ce shi ne yayi nasara a zaben gwamnan Kano na 2023 Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bukaci magoya bayansa da su ƙara dagewa da addu’o’i domin samun nasara a kotun ƙolin.
Alfijir Labarai ta rawaito Gawuna ya faɗi haka ne ta Cikin wani sako da ya sanyawa hannu da kansa.
Yayi godiya ga shugaban jamiyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano Dr. Abdulkahi Umar Ganduje bisa yadda ya yita kokarin ganin sun samu nasara a kotu.
Nasiru ya kuma yabawa magoya bayan jamiyyasa APC a kano bisa yadda suka jajirce.
Ya kuma godewa alummar Kano bisa irin kyakykyawan zaton da suke yi masa.
“Ina godewa kotun daukaka kara saboda yadda tabbatar da gaskiya ta hanyar jaddada hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar kano ta yanke tun ranar 20 ga watan Satumbar wannan shekara”. Inji Gawuna
Ya kara da cewar, abun da alkalan kotun nan tirabunal da kotun daukaka kara sukai na tabbatar da gaskiya cigaba ne ga dimokuradiyya, sannan kuma hakan ya nunawa duniya cewa kotu ita ce gatan mara gata.
“Ina godiya tare da yabawa mataimakin Shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibril da Ministocinmu guda biyu da shugaban jam’iyyar APC na jihar kano Abdullahi Abbas , sai Malamai yan kasuwa da duk al’ummar jihar kano bisa goyon bayan da suka bamu har muka sami wannan nasarar “. A cewar Dr. Nasiru Gawuna
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp