Sakon Gwamnan Kano Abba Kabir Ga Nasiru Yusif Gawuna

IMG 20240112 WA0302

Gwamnan kano Abba Kabir Yusif, ya bukaci dan takarar gwamnan kano a jam’iyyar APC Nasiru yusif gawuna, yazo su hada kai domin ciyar da kano gaba.

Alfijir labarai ta rawaito Gwamnan ya bukaci hakan ne, a yayin da yake jawabi ga manema labarai, jim kadan bayan futowa daga kotun koli.

Abba yace, hukuncin kotun kolin ya kawo karshen takaddamar da akeyi akan zaben daya gudana a ranar 18 ga watan Maris din shekarar data gabata.

Haka kuma gaskiya tayi halinta, duba da yadda kotun koli ta tabbatar wa da Al’ummar kano abin da suka zaba.

Domin haka Abba yace ya kamata Gawuna yazo su hada kai, domin su kai kano matakin da zata zama abin kwaikwayo, a tsakanin kasashen duniya.

A karshe zababben gwamnan na kano yace, kofa a bude take ga dukkan bangaren ‘yan adawa domin suzo a ciyar da kano gaba, tunda dukkan su fatan da suke yi wa kano kenan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

2 Replies to “Sakon Gwamnan Kano Abba Kabir Ga Nasiru Yusif Gawuna

  1. GASKIYA NAJI DADIN BAYANIN GWAMNAN KANO ABBA KABIR YUSIF,KUMA NA GAMSU DA ABINDA YA FADA IDAN HAR GASKIYA NE KANO CE A GABAN SU,YA KAMATA SU HADA KARFI DA KARFI DAN SU KAWO CIGABA A FADIN JAHAR KANO DA KEWAYE,FATAN ALKHAIRI GA JAHAR KANO

  2. GASKIYA NAJI DADIN BAYANIN GWAMNAN KANO ABBA KABIR YUSIF, KUMA NA GAMSU DA ABINDA YA FADA, IDAN HAR GASKIYA NE KANO CE A GABAN SU, YA KAMATA SU HADA KARFI DA KARFI DAN SU KAWO CIGABA A FADIN JAHAR KANO DA KEWAYE FATAN ALKHAIRI GA JAHAR KANO

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *