Shugaba Najeriya Bola Tinubu ya amince da nadin jarumi Ali Nuhu a matsayin Manajan Darakta na Hukumar tace Fina-Finai ta Najeriya da wasu mutane goma a matsayin shugabannin hukumomin da ke karkashin ma’aikatar fasaha, al’adu, da tattalin arziki.
Alfijir labarai ta rawaito hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a.
Sauran sun hada da:-
(1) Tola Akerele — Director-General, National Theatre
(2) Dr. Shaibu Husseini — Director-General, National Films and Censors Board
(3) Mr. Obi Asika — Director-General, National Council for Arts and Culture
(4) Aisha Adamu Augie — Director-General, Centre for Black and African Arts and Culture
(5) Ekpolador-Ebi Koinyan — Chief Conservator, National War Museum
(6) Ahmed Sodangi — Director-General, National Gallery of Art
(7) Chaliya Shagaya — Director-General, National Institute of Archeology and Museums Studies
(8) Hajiya Khaltume Bulama Gana — Artistic Director, National Troupe of Nigeria
(9) Otunba Biodun Ajiboye — Director-General, National Institute for Cultural Orientation
(10) Ramatu Abonbo Mohammed — Director-General, National Commission for Museums and Monuments
A cewar sanarwar, “Shugaban kasa ya umurci wadanda aka nada su gudanar da ayyukansu bisa ka’idojin kwarewa, kwazo, da kishin kasa da nufin ganin bangaren ya kara mitsawa da kwarjini.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl