Ku Ajiye Bambancin Siyasa ku Fuskanci Al’ummarku
Alfijir labarai ta rawaito shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su ajiye bambancin siyasa a gefe su hada kai da gwamnatin tarayya wajen gina kasa.
Tinubu ya yi wannan kiran ne a lokacin bude-bakin azumin watan Ramadan tare da gwamnoni a fadar gwamnati da ke Abuja, a jiya Alhamis.
Ya kuma jaddada muhimmancin ajiye siyasa a fuskanci mulki, inda ya ce akwai bukatar hadin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki.
“Tunda mun fahimci bukatar gina al’ummarmu tare, lokacin siyasa ya wuce. Yanzu lokaci yayi na mulki.
“Mu ‘yan uwa daya ne kuma iyayenmu daya; mu na zaune a gida daya, amma a dakuna daban-daban mu ke kwanciya. Dole ne mu hada kai da yada soyayya a tsakanin juna,” inji shi
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk