Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Roki ‘Yan Kasuwa Su Rage Farashin Kayan Abinci Darajar Ramadan

FB IMG 1709422107907

A wajen kaddamar da littafin tarihin “Daulolin Kasar Hausa” wanda Farfesa Sa’idu Muhammed Gusau ya wallafa, Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi kira na musamman ga’ yan kasuwa da su sassauta kan farshin kayan abinci da ragowar kayan masarufi.

Alfijir labarai ta rawaito an yi taron ne a masarautar Zazzau, ranar Lahadi, in da Sarkin Kanon ya nuna irin alheran da ‘yan kasuwa za su samu daga Allah, idan su ka tausayawa bayinSa a wannan wata mai alfarma na Ramadhan.

Haka kuma ya kara yin kira ga mawadatan cikin al’umma da su taimakawa talakawa ganin yadda rayuwa ta kara zama a matse.

“Ina rokon’ yan kasuwar mu kamar yadda na saba kan su dubi irin taimako da dauki da albarka da za su samu daga Mahaliccinmu idan su ka rage farashin kayan abinci da ragowar kayan masarufi. Musamman ganin kusantowar wata mai Alfarma na Azumin Ramadhan,” in ji Sarkin.

Ya ce” Mu na rokon mawadatanmu da su taimakawa al’umma wajen rage musu radadi na wannan rayuwa. Cikin sahalewar Allah.”

Sarkin ya yabawa Farfesa Gusau wajen fito da tarihin Daulolin Kano da Sakkwato da Zazzau da Zamfara da Katsina da Kebbi

An yi sowa sosai lokacin da Sarkin yake wannan kiran da yake nuna tausayi da son al’umma dake zuciyar Sarkin. Kamar yadda wasu jama’a da mu ka tattauna da su suka fada jim kadan bayan tashi daga taron.

Mawallafin littafin Farfesa Gusau ya godewa Mai Martaba da duk iyayen kasa da su ka halarci taron.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *