Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf murnar nasarar da ya samu a kotun koli.
Alfijir labarai ta rawaito Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya ce hukuncin kotun koli nuni ne na zabin mutane da kuma dimokuradiyya da kuma shugabanni na kwarai da masu biyayya ga abin da masu zabe za su yi.
“A cewar sanarwar dake kunshe ta taya murna, Sarkin ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa zabin da ya dace wanda zai tabbatar da ci gaba da tsare-tsare na cigaban jihar.”
Daga karshe ya yi addu’ar Ubangiji Allah ya kare shi daga makiya na zahiri da badini, ya kuma ba shi kwarin guiwar cika alkawura da kuma gudanar da ayyukansa cikin himma da nasara.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V