Sarkin Kano Sanusi II Yayi Raddi Game Da Maganar Taka Sunan Muhammadu

Sarki Sanusi II

Sarki Sanusi Lamido Sanusi na II, yayi taddi ga masu sukarsa game da kafet din dake dauke da sunansa, in da yace Khalifa Muhammad Sanusi Lamido Sanusi Sarkin Kano aka saka ba wai Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wassalam ake nufi ba.

Alfijir Labarai ta rawaito Sarkin ya kawo nassi da fahimtarsa game da irin saka sunan, ya kuma Kawo hujjar cewa in dai ba Muhammad Salallahu Alaihi Wassalam aka saka ba ko a jingina wani sunan dake nuni da martabar Annabi babu kuskure dan an saka suna domin da manufar da take nuni da Annabi ake.

Ban take sunan Annabi Muhammadu a kafet dina ba, domin sunana ne a jiki, kuma duk me ganin yana da hujjar da tafi tawa a shirye nake dana bi maganarsa. Cewar Lamido

Daily News Hausa 24

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

One Reply to “Sarkin Kano Sanusi II Yayi Raddi Game Da Maganar Taka Sunan Muhammadu”

  1. Shi gyara idan aka Yi Maka duk Ilimin ka Yana da kyau ka dauki gyaran, Malamai sun ce ko Kiran Mai sunan Muhammad za ka Yi to ka Yi shi cikin ladabi da kyautatawa, saboda darajar Mai sunan. Anan ba maganar sunan ka ba ne ko wani Abu darajar sunan ne yasa aka ce Bai kamata a rubuta shi a kasa yadda za ake takawa ba. Babu Kari Babu dadi aciki. Suna ba naka ba ne copywrite ne aka Saka Maka sunan Mai darajar da daukaka, da kamar sunan lamidon ne kawai Babu Wanda zai ce Maka komai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *