Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ”nan ba da jimawa ba za mu buɗe mashigar Hormuz ko ta halin ƙaƙa”, don jirage su wuce cikin kwanciyar hankali.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce yana fatan China da Faransa da Japan da Koriya da Kudu da kuma Birtaniya za su aika jiragen ruwa na yaƙi zuwa mashigar ”domin kare duk wata barazana” daga Iran.
Ya ƙara da cewa ƙasasashe da dama za su aika jiragen ruwansu na yaƙi domin tabbatar da ”tsaro a mashigar”
Ya ce a yanzu Amurka za ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai kan jiragen ruwan Iran da ke wajen mashigar”.
Ya yi iƙirarin cewa Amurka ta ”lalata kashi 100 na ƙarfin sojin Iran, amma ya ce takan yi amfani da jirage marasa matuƙa da dasa nakiyoyi da kuma makamai masu linzami masu cin gajeren zango.
Wakilin Iran a Geneva, Ali Bahrani ya ce iƙirarin Trump ɗin na lalata ƙarfin sojin Iran ”ƙirƙirarren labari ne”.
BBC
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t