Saudiyya ta ƙara Yawan Maniyyatan Hajjin bana Ta Kuma Rage a Yawan Shekaru Masu Zuwa Hajjin

Alfijr

Alfijr ta rawaito Kasar saudiyya ta ƙara yawan adadin Maniyyatan hajjin bana zuwa miliyan ɗaya daga cikin ƙasar da kasashen duniya, kamar yadda shafin Haramain ya wallafa a tweeter.

Ma’aikatar kula ayyukan Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ce ta sanar da matakin ƙara yawan masu aikin Hajjin hajjin zuwa miliyan daya daga ciki da wajen Saudiyya.

Idan aka kwatanta da shekaru biyu da suka gabata, za a ga an sami karuwar adadi, saboda annobar korona wanda ya tilasta rage yawan waɗanda za su aikin Hajji.

Alfijr

Daga bisani kuma sanarwar ta kara da cewar an hana wa waɗanda suka haura shekara 65 zuwa aikin Hajjin bana, sannan kuma y’an ƙasa da shekara 65 da za a bari su yi aikin Hajjin sai sun yi allurar rigakafin korona da ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta amince da ita kafin barinsu su shiga kasar.

Slide Up
x