Sayen Kuri’u 2023: Za Mu Toshe Asusun Gwamnati A Farkon Watan Janairu

Alfijr ta rawaito NFIU A kokarinta na dakile sayen kuri’u a babban zaben shekara mai zuwa, sashin kula da harkokin kudi na Najeriya (NFIU) ya ce za a toshe dukkan asusun gwamnati a farkon watan Janairu, inda za a bar kudi kawai domin biyan albashin ma’aikata da gudanar da ayyukan yau da kullum na ma’aikatu da sassan da hukumomi (MDAs).

Kazalika, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’anta suna kokarin ganin an hana yin amfani da kudi ya yi tasiri a zaben 2023 ko kuma a ce an kawo karshen wannan matsala.

Shugabannin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, a wani taron masu ruwa da tsaki na yini daya da aka yi a Abuja ranar Litinin, sun yi tir da illar sayen kuri’u ga zabukan kasar.

Taron wanda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shirya, tare da rundunar ‘yan sandan Nijeriya (NPF), da
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Hukumomin Laifuka (ICPC), da sauran su.

Majalisar Dokokin Tallace-tallace ta Najeriya (APRCON), ita ce ta magance tasirin kudi a babban zaben 2023.

Darakta Janar na Hukumar NFIU Modibbo Turkur, ya ce galibin mutanen da ke sayan kuri’u na yin hakan ne saboda kudaden da suke da su kyauta.

Turkur ya ce NFIU za ta yi aiki tukuru a kan dukkan ‘yan siyasa da kuma asusun jam’iyyun siyasa.

“Tare da kunnawa da kuma kafa asusun ajiyar, duk wani janyewar za a sanar da shi kuma za a aika da rahoton ga hukumomin da suka dace don daukar mataki.

“Ba mu kama ba, amma ku tabbata cewa za mu sanya ido a kan duk yadda ake cire makudan kudade da aka yi a lokacin zaben.

“Za mu kuma fitar da asusun ‘yan takarar jam’iyyun siyasa da sauran su a karkashin kulawarmu.

“Za kuma mu karfafa manufofin CBN, kuma idan tattalin arzikin da ba na tsabar kudi ba, ba za a yi taho mu gamu ba.

Tukur ya ci gaba da cewa hukumar NFIU a halin yanzu tana binciken sama da mutane 15,000 na asusun gwamnati.

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usma Alkali Baba, ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya a matsayinta na kan gaba wajen gudanar da harkokin tsaro a zaben, za ta tura jami’an X-Squad da jami’an leken asiri da kuma masu bincike zuwa filin domin tabbatar da cewa ‘yan siyasar da ke tafiya ranakun zabe tare da kudi na zahiri domin sayen kuri’u, an kama su, kuma an yi mu’amala da su bisa tanadin doka.

IGP, wanda ya samu wakilcin Mataimakin Sufeto Janar (AIGOperations) Bala Ciroma, ya bayyana cewa rundunar ta tura jami’an leken asiri wadanda za su “shiga cikin jama’a” a yayin tarukan siyasa domin gano madu tada zaune tsaye.

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya yi kira da a bayyana cikakken duk wasu kudaden da aka ware domin yakin neman zabe na jam’iyyun siyasa.

Bawa wanda ya samu wakilcin shugabar ma’aikatan fadar sa, Hadiza Gamawa, ya tunatar da ‘yan siyasa cewa dokar zabe ta tanadi daurin shekaru 14 a gidan yari saboda saba duk wani tanadin dokar.

A nasa bangaren shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya yi tir da illar da sayen kuri’u ke yi a harkar zabe.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *