Sanata Ali Ndume, ya ki amincewa da nadin da aka yi masa a matsayin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yawon bude ido. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi wa Ndume sabon mukami ne biyo bayan tsige shi daga mukamin babban mai Tsawatarwa na majalisar dattawa ta 10. Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sun bukaci Akpabio da ya tsige Ndume saboda sukar da ya yi wa Shugaba Bola Tinubu a kwanakin baya.
Alfijir labarai ta ruwaito da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a yau Juma’a, Ndume ya kare matakin da ya dauka, inda ya ce bai yi nadama ba.
“Game da tsige ni a matsayin shugaban kwamitin kasafin kudi, ba ni da rai a kan lamarin, an shawo kan ni na karbi mukamin babban mai Tsawatarwa tare da sanin cewa na jagoranci yakin neman zaben Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa, ni ma an ba ni dama. in zabi kwamitin da nake so kuma na zabi mataimakin shugaban kwamitin kasafin kudi.
“Na samu labarin cewa an nada ni shugaban kwamitin yawon bude ido, amma ban samu wata sanarwa a hukumance ba. Ina so in bayyana karara cewa na ki amincewa da wannan tayin saboda dalilai guda biyu: Ni ba dan yawon bude ido ba ne kuma ba ni da sha’awar yawon bude ido.
Ndume ya kuma bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tunkari batutuwan da ya gabatar inda ya jaddada cewa talakawa na cikin wahala.
“Ba kishin kasa ba ne a goyi bayan shugaban kasa ba tare da wani sharadi ba, gaskiya kishin kasa ya hada da fadin gaskiya, ba wai ga shugaban kasa kadai ba har ma ga duk wanda ke rike da madafun iko, rashin kishin kasa ne a boye gaskiya, a kasar Hausa mu ce Allah ya yi tare da mai gaskiya. ‘ ma’ana Allah a koyaushe yana tare da masu gaskiya.
“Na san ba ni da kuskure, jama’a ba su yi kuskure ba don fadin gaskiya da tsayawa a kan ta, ina sa ran Shugaban kasa ya yi la’akari da kalamai na kuma ya dauki matakan da suka dace don rage radadin da ake ciki.
“Mutane ba su ji dadi ba, suna shan wahala, suna fushi, ya kamata shugabannin kasar nan su sake duba ayyukansu, su magance matsalolin da na taso, Allah ne ya ba ni wannan matsayi, kuma Allah ne ya dauke shi, ba ni da hurumi a kan haka. Bayan haka, ban yi takarar zama babban mai Tsawatarwa ko mataimakin shugaban kwamitin kasafin kudi ba;
“Alhamdulillah, Allah ya bani nasara, kuma na kasance tare da Allah.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj