Shugaba Buhari ya sha kaye a Kotun Ƙoli kan Dokar Zaɓe Ta 2022

Alfijr

Alfijr ta rawaito kotun Koli a Nijeriya ta yi watsi da ƙarar da Shugaba Muhammadu Buhari da Babban lauyan gwamnati suka shigar, suna bukatar fashin baki kan sashe na 84 na dokar zabe ta 2022 da aka yi wa garambawul.

Sashen ya haramata wa duk wani mai rike da mukami na siyasa, da aka nada a dukkan matakai, ya kada kuri’a a zaben fitar da gwani na duk wata jam’iyya.

Alkalan Kotun bakwai da suka yi zaman ranar Juma’a a karkashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dattijo, dukansu sun amince cewa karar yunkurin wahalar da kotu ne kawai.
Alfijr

A hukuncin da Mai Shari’a Akomaye Agi ya karanto, Kotun Kolin ta ce ba zai yiwu Shugaba Buhari ya nemi a goge sashen na 84 da dokar zabe 2022, bayan da a baya ya aminta da shi.

”Shugaban kasar ba shi da ikon bukatar majalisa ko tursasa ta ta sauya wani abu a dokar da a baya ya bada hadin kai ya kuma aminta da shi,” in ji shi.

Alfijr

Karar ta biyo bayan hukuncin wata kotu a birnin Umuahia a jihar Abia, wadda ta soke sashe na 84 (12)karamin sashe na 122

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa

Slide Up
x