Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa da duniya a Hadaddiyar Daular Larabawa cewa Najeriya a shirye take ta hada kai da sauran kasashe domin gina kasa mai juriya, daidaito da kuma dorewa.
Shugaba Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a rana ta biyu na makon nemo hanyoyin Dorewar makamashi maras illa da ake gudanarwa Abu Dhabi na 2025 akan “Daga Mahimmancin yanayi zuwa Ci gaban Tattalin Arziki.
Shugaban ya bayyana cewa, babu wata kasa guda da za ta iya tafiya a kan hanyar dorewar ita kadai, yana mai jaddada cewa, cudanya da juna a duniya na bukatar daukar matakai na bai daya, da kuma goyon bayan juna.
“Yakin da ake yi da sauyin yanayi ba wai wata bukata ce kawai ta muhalli ba, amma wata dama ce ta tattalin arzikin duniya don sake fasalin yanayin nahiyarmu da yanayin makamashin duniya.
“A matsayinmu na shugabanni, masu ruwa da tsaki da kuma ‘yan kasa na wannan duniyar tamu, mun tsaya a wani muhimmin lokaci a tarihin dan Adam. Don samun nasara, dole ne mu kirkiro sabbin abubuwa, hada kai da kuma yin aiki mai tsauri a matsayin al’ummar duniya daya,” in ji shi.
Da yake nanata kudurin gwamnatinsa na rage hayakin Carbon, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa mahalarta taron cewa, gwamnatin Najeriya ta samar da shirye-shirye masu dacewa daidai da abin da ake tsammani a duniya, tare da la’akari da hasashen tattalin arziki da siyasar Najeriya.
Shugaba Tinubu ya yabawa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohamed bin Zayed bin Sultan Al Nahyan, bisa gayyatar da yayi da kuma hangen nesa wajen shirya taron.
Taron ya tattaro shugabannin duniya tare don yin musayar ra’ayi da ra’ayoyi kan yadda za a magance kalubalen duniya na zamaninmu tare.
RN
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj