Shugaba Najeriya Zai Kaddamar Da Masana’antun Iskar Gas Uku A Najeriya

IMG 20240504 WA0004

Shugaban is Kasa Bola Ahmad Tinubu na shirin kaddamar da wasu masana’antun sarrafa iskar gas guda uku wadanda za su bunkasa samar da iskar gas ga kasuwannin cikin gida a ƙasar nan.

Alfijir Labarai ta rawaito shirin wanda zai kai kubik miliyan 500 a kowace rana, tare da kuma inganta zuba jari a kasar.

Ayyukan, waɗanda Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) da abokan hadin gwiwa ke gudanarwa, za a yi su ne don tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin tarayya na inganta darajar ɗaga kadarorin iskar gas na ƙasa tare da rage hayaƙin ƙona iskar gas.

An bayyana hakan ne a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale.

Ya bayyana cewa, an hanzarta kai ayyukan tun daga farkon gwamnatin Shugaba Tinubu wajen ɗorewar manufar zurfafa samar da iskar gas a cikin gida a matsayin hanyar bunkasa tattalin arziki.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *