Shugaba Tinubu Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga Matasan Nigeria Kan Zanga-zanga

IMG 20240709 WA0188

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su dakatar da zanga-zangar da suka shirya yi a watan Agusta.

Alfijir labarai ta ruwaito ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce Tinubu yana son masu shirya zanga-zangar su jira martanin gwamnati game da damuwarsu, zanga-zangar da ake gangaminta a Intanet, an shirya yinta ne a watan Agusta kuma za a yi ta ne a duk jihohin Najeriya da babban birnin tarayya, Abuja, sai dai har ya zuwa yanzu ba a san waɗanda ke shirya zanga-zangar ba.

’Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar kayan abinci da kayan masarufi saboda matsalolin tattalin arziki sakamakon cire tallafin man fetur da sauye-sauye ga manufofin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje da gwamnatin Tinubu ta yi.

Gwamnatin ta hannun hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa (NOA), da rundunar ‘yan sandan Najeriya, da majalisar wakilai, sun yi gargaɗi game da zanga-zangar.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) da Sanata Ali Ndume sun buƙaci shugaban ƙasa da ya magance matsalolin da matasa suka gabatar.

Kakakin fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya yi gargaɗin cewa zanga-zangar na iya rikiɗewa zuwa tashin hankali da kuma yin ɓarna kamar yadda aka yi a zanga-zangar EndSARS a watan Oktoban 2020, lamarin da ya kai ga asarar dukiya mai tarin yawa.

Ministan ya ce shugaba Tinubu yana aiki tukuru domin ganin ya cika bukatun al’umma, don haka ya ce babu bukatar matasa sai sun gudanar da zanga-zanga.

” Ba wai muna tsoron ayi mana zanga-zanga ba ne, kawai dai bata cika haifar da da mai ido ba, yanzu ku kalli abun da ya faru a kasashen Sudan,Libiya da dai sauransu, dukkanin su a Sanadiyyar zanga-zanga suka tsinci kawunan su a halin da suke ciki”.

Ya ce shugaba Tinubu ya Dukufa don ganin an baiwa matasan Nigeria tallafin karatu don inganta rayuwar su, da kuma ba tun mafi ƙarancin albashi dukkanin su Shugaba Tinubu ya samar da kudaden da za a gudanar da wannan aikin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *