Daga Aminu Bala Madobi
Shugaban mulkin soja a kasar Gabon Brice Claitoire Nguema ya gayyaci Hamshakin Dan kasauwa Alhaji Aliko Dangote domin kafa masana‘antu a kasar ta Gabon.
Alfijir Labarai ta rawaito Brice Nguema yace zuwan Dangote kasar Gabon zai taimaka matuka wajan bunkasa tattalin arzikin kasar la’akari da abinda ke faruwa dashi a Najeriya.
Wannan na zuwa ne a gabar da hukumomi na bangaren man fetur a Najeriya ke cigaba da kalubalanta da jan-cunar wandon dan kasuwar dangane nasarar da yayi na kafa masa’antar fetur.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar kula da man fetur ita ce ke ci gaba da caccakar Dangote tare da alakanta kayan da kamfanin ya fara tacewa a matsayin marasa inganci.
Hamshakin attajiri a nahiyar Afirka Dangote, ya ce daya daga cikin abokansa da ya fara zuba jari a kasashen waje shekaru hudu da suka wuce, yana yi masa gori a baya a ‘yan kwanakin nan.
Tun da farko Dangote ya ba da labarin yadda wani ke kokarin toshe hanyoyinsa na shigo da danyen mai da kuma yadda ake samun wahalar kayayyakin cikin sauki.
Sai dai a makon da ya gabata, hukumar kula da man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ce har yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta ba wa matatar man Dangote lasisin fara aiki a kasar ba.
Farouk Ahmed, babban jami’in gudanarwa na hukumar NMDPRA, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis.
A cewar Ahmed, ikirari da ake yi na durkusar da ayyukan matatar ta Dangote sakamakon rashin samar da danyen mai da kamfanonin mai na kasa da kasa ke yi ba gaskiya ba ne, ya kara da cewa matatar ta na nan a matakin farko kuma har yanzu ba a ba ta lasisi ba.
Ahmed ya kara da cewa man Dizal din Dangote bai kai matsayin kasa da kasa ba, lamarin da dan kasuwar ya musanta a wata tattaunawa da yayi a karshen mako.
Rayuwar duniya kenan…
Idan wani ya kika da wuni wani da Kwana zai so ka