Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake nada Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na wani sabon wa’adi na shekaru biyar.
Marwa, wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a watan Janairu 2021, zai ci gaba da jagorantar hukumar har zuwa shekara ta 2031. Kafın wannan, ya jagoranci Kwamitin Shugaban Kasa kan Kawar da Shan Miyagun Kwayoyi daga 2018 zuwa 2020.
Tsohon hafsan soja ne dan asalin jihar Adamawa, kuma ya taba zama gwamnan soji na jihohin Legas da Borno. Marwa ya yi karatu a Makarantar Soja ta Najeriya da kuma Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA).
Sanarwar ta fito ne daga Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan yada labarai.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t