Gwamnan Kano ya kaddamar da rukunin dalibai su 590 da za su amfana da shirin tallafin karatun digiri na biyu

Abba k Yusuf

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da zagaye na biyu na dalibai 590 da za su amfana da shirin tallafin karatun digiri na biyu na 1,001 Postgraduate Foreign and Domestic Scholarship Programme na gwamnatin jihar.

Yayin bikin kaddamar da shirin da aka gudanar a Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wannan shirin na bayar da guraben karatu, wanda Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya fara a baya, gwamnatin sa ta farfado da shi ne domin gina ƙwarewar ilimi da sana’ar matasan Kano, a gida da waje.

Gwamnan ya Kuma tunatar da cewa dalibai 418 ne suka ci gajiyar zagaye na farko na shirin, wanda ya lashe kimanin Naira biliyan 5, kuma duk sun kammala karatunsu cikin nasara, wasu ma sun samu ayyukan yi a ƙasashen waje.

“Wannan zagaye na biyu da ya ƙunshi dalibai 350 da za su tafi ƙasashen waje da dalibai 240 da za su yi karatu a jami’o’in cikin gida wata gagarumar nasara ce a kokarinmu na gina matasan da za su zama ginshikin ci gaban jihar Kano.

Ya Kara da taya sabbin daliban murnar samun wannan dama ta musamman bisa cancanta da kyawawan halaye, yana mai kira gare su da su kasance masu jajircewa, ladabi, da wakiltar jihar Kano da Najeriya cikin nagarta a duk inda suka tsinci kansu.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya tabbatar musu da sauƙin tafiya da nasarar karatu, tare da tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bai wa ilimi muhimmanci a matsayin ginshiƙin ci gaba, kirkire-kirkire, da walwalar al’umma.

Haka kuma, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa shirin tallafin karatun yana cikin jerin sauye-sauyen da gwamnatin sa ta kawo a fannin ilimi, wanda ya sa aka ware kashi 31 cikin 100 na kasafin kudin 2025 ga fannin ilimi mafi girma a tarihin jihar Kano.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *