Shugaba Tinubu Ya Janye Nadin Da Ya Yi Wa Matashi Shugabancin FERMA

FB IMG 1697751231569

Shugaba Tinubu, ya bayar da umarnin janye sunan Injiniya Imam Kashim Imam daga nadin da ya yi masa a matsayin shugaban Majalisar Daraktocin Hukumar Gyaran Hanyoyi ta Tarayya (FERMA).

Alfijir Labarai ta rawaito hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar  ranar Alhamis.

Ya ce“Umarnin janye sunan zai fara aiki ne nan take. Sai dai duk sauran nade-naden da aka yi na hukumar gudanarwar hukumar ta FERMA na nan daram,” in ji sanarwar.

Nadin matashin dai shekara 24 a makon da ya gabata ya janyo ce-ce-ku-ce matuka a fadin Najeriya.

Yayin da wasu suke jinjina masa kan nada matasa, wasu kuma sun soki lamirinsa kan nada wanda sam ba shi da wata kwarewa ya jagoranci hukumar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *