Kotun Koli ta sanya ranar Litinin 23 ga watan Oktoba, don fara sauraron karar da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, babbar mai adawa a Najeriya, ya daukaka a kan zaben 2023.
Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa da magatakardar kotun Zainab M Garba ta sanya wa hannu, ta zayyana hukumar zabe ta INEC da wasu, a matsayin wadanda ake kara.
Atiku Abubakar dai ya yi alkawarin daukaka kara ne a kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe na ranar 6 ga watan Satumba da ya tabbatar da nasarar Bola Tinubu.
Jagoran adawar na Najeriya ya samo ƙarin shaida a kan karar da ya shiga yana kalubalantar cancantar Tinubu, inda yake fatan Kotun Kolin za ta ba shi damar gabatar da ita, yayin da take sauraron shari’arsa.
Hukumar zabe ta INEC ta ayyana cewa Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya samu kuri’a 8,794,726, yayin da ta ce Atiku Abubakar ya samu kuri’a 6,984,520.
Sai dai a karar da ya daukaka gaban Kotun Kolin, Atiku ya shigar da hujjoji guda 35, wadanda yake cewa bisa la’akari da su, kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a karkashin Mai shari’a Haruna Tsammani ta “tafka babban kuskure”.
A takardar daukakar da babban lauyan dan takarar na PDP, Chris Uche ya shigar, Atiku Abubakar ya roki kotun ta jingine duk abubuwan da kotun zaben shugaban kasa ta gano da kuma matsayar da ta cimma.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo