Shugaba Bola Tinubu Ya jaddada Cewa ya Kamata a ɗauki Mutanen da ke yin Garkuwa da Mutane a Matsayin ‘yan ta’adda.
Alfijir labarai ta rawaito shugaban yace, ”Dole ne mu ɗauki masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda.
Suna zuwa makarantu suna sace yara suna haifar da rashin jituwa. Dole ne mu dauki su daidai a matsayin ‘yan ta’adda, domin mu kawar da su, Kuma na yi muku alƙawarin za mu kawar da su.”
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin liyafar cin abincin dare da ya samu halartar jami’an hukumar shari’a da wadanda suka yi ritaya, ciki har da tsofaffin alkalan kotunan guda biyu, Mai shari’a. Mahmud Mohammed da Justice Walter Onnoghen.
Kamar yadda mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya wallafa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk