Shugaba Tinubu Ya Sauke Sha’aban Sharada Ya kuma Nada Wasu Yan Kano Mukamai

FB IMG 1710375660100

Tinubu ya sauke Sha’aban Sharada daga mukamin da Buhari ya bashi, tare da maye gurbinsa da dan Kano

Alfijir labarai ta rawaito shugaban Najeriya ya amince da nadin Birgediya-Janar Lawal Ja’afar Isa (Rtd) a matsayin Babban Sakataren hukumar kula da Almajiri da yaran da basa zuwa makarantar ta kasa.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da nadin Alhaji Tijjani Hashim Abbas a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin masarautu.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu.

Shugaban Yayi fatan sabbin wadanda aka nada din za su yi amfani da gogewar da suke da ita wajen gudanar da ayyukan da aka dora musu don cigaban al’ummar Nigeria.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *