Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci karamin ministan tsaro Bello Matawalle ya koma jihar domin sanya idanu kan ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar ke yi na ceto ɗaliban.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Alhamis ta ce ministan zai isa jihar Kebbi a yau Juma’a bisa umarnin shugaban ƙasa.
Tun farko shugaba Tinubu ya aika mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima zuwa jihar domin jajanta wa iyayen ɗaliban tare da ganawa da al’umar yankin da kuma bayyana musu irin matakan da gwamnati ke ɗauka ]wajen kuɓutar da ɗaliban.
A farkon wannan mako ne wasu ƴan bindiga riƙe da muggan makamai suka shiga makarantar Sakandiren ƴanmata da ke gari Maga a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar tare da sace ɗalibai 24.
Tun bayan umarnin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bai wa ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle na komawa jihar Kebbi domin taimaka wa yunƙurin ceton ɗaliban da ka sace, ƴan ƙasar ke ta magana kan irin da rawar da zai taka.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t