“Shugaba Tunibu ya tabbatarmin da za’a mallakawa mutanen unguwar Rimin Zakara Muhallansu

FB IMG 1738777561224

Daga A’isha Salisu Ishaq

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero OFR, yayi wata ganawa ta sirri da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu mintina kadan kafun tashinsa zuwa taron AU da za’a gudanar a Adis ababa dake kasar Ethiopia.

Alfijir labarai ta rawaito ganawar da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi da shugaban kasar tana da nasaba ne da iftila’in daya faru ga al’umar Rimin Zakara dake yankin Karamar Hukumar Ungogo a jihar Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace Shugaban kasa ya tabbatar masa da cewar za’ayi duk mai yuwuwa domin ganin an warware takaddamar tareda tabbatar musu da matsugunansu.

Wannan na kunahe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sahannun Abubakar Balarabe Kofar Naisa Sakataren yada labarai na sarkin.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *