Shugaban Amurka Donald Trump ya rufe gidan radiyon Muryar Amurka, VOA

FB IMG 1742148617718

Shugaba Trump ya ɗauki matakan dakatar da ma’aikatan kafar yaɗa labaran Amurka ta VOA da sauran rassanta da suke aiki tare wajen yaɗa shirye-shirye a faɗin duniya.

Alfijir labarai ta rawaito cewa Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani.

Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya.

Babu dai wani takamaiman bayyani daga gwamnatin Amurka kan me hakan ke nufi, sannan babu wanda zai iya fahimtar ko an rufe kafofin baki ɗaya ke nan.

Shugaban ƙungiyar ƴan jarida a Amurka, William McCarren ya ce wannan ba abin alheri ba ne ga duniya da kuma aikin jarida baki ɗaya, musamman a wannan zamani da ake yaƙi da labaran bogi.

Kafar VOA ko Muryar Amurka na yaɗa shirye-shiryenta ga masu sauraro sama da miliyan 400 a sassan duniya, kuma girmanta ɗaya da BBC, ta gwamnatin Burtaniya.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *