Shugaban APC Ya Magantu Kan Batun Sulhu Tsakaninsu Da NNPP A Kano

FB IMG 1702885190749

Jam’iyyar APC a Kano ta ce babu wata maganar sulhu da aka cimma dangane da hukuncin kotu tsakaninta da jam’iyyar NNPP.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban jam’iyyar APC na jihar kano Abdullahi Abbas ya sanar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar a ranar lahadi a Abuja,

Sanarwar tace ba gaskiya bane, jita-jitar da wasu magaoya bayan NNPP ke yadawa na cewar shugaban Kasa Bola Tinubu ya shiga tsakani domin tabbatar da kujerar gwamnan kano ga jam’iyyar NNPP, daga bisani zasu koma APC.

Sanarwar ta kara da cewar jam’iyyar NNPP ta kirkiri waccan jita-jitar ne domin dauke hankalin magoya bayanta, ta yadda zai zama sun dada samun kwarin gwuiwar gwamnatin su zata dore.

Abdullahi Abbas yace babu wanda ya zauna da shugaba Tinubu ko wani jigo a jam’iyyar APC, dangane da maganar yin sulhu da NNPP.

Kuma shi Tinubu gogaggen dan Siyasa ne, wanda yasan ka’idojinta da kuma abubuwan da Suka dace da ita, dan haka bazai goyi bayan wadanda aka ce sun ci zabe ta hanyar satar kuri’a ba.

Abbas yace jam’iyyar su ta APC tana da kwarin gwuiwar kotun koli zata tabbatar da nasararsu, duba da yadda kwararan hujjojinsu, suka basu nasara a kotunan baya.

A karshe sanarwar tayi fatan yan jam’iyyarsu dama al’ummar Najeriya za suyi watsi da jita-jitar da NNPP Take yadawa, a kokarinta na kawo hargitsi a jahar Kano.

FB IMG 1702885198678
Press Realise
FB IMG 1702885201600
Press Realise

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *