Shugaban INEC Zai Bayyana Gaban Kotun Korarrakin Zabe Kasar


Alfijir Labarai ta rawaito shugaban hukumar zabe mai zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmoud Yakubu zai gurfana a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ranar Alhamis.

Wannan ya fito ne a ranar Talata daga bakin

Babban Lauyan Atiku Abubakar Chris Uche, SAN ne ya bayyana haka a ranar Talata da ta gabata a karar da suke ci gaba da yi.

Alfijir ta tattaro, a wata kara mai lamba CA/PEPC/05/2023, Abubakar Atiku da jam’iyyar PDP na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu wanda ya ayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Wadanda ake kara sun hada da hukumar zabe mai zaman kanta INEC, da shugaban kasa Bola Tinubu da kuma jam’iyyar APC.

Uche SAN ya ce shugaban hukumar ta INEC a lokacin bayyanar sa zai ba da shaida kan yadda zaben shugaban kasa ya gudana

Ya kuma shaida wa kotun cewa ba ya son a gabatar wadanda ake kara musamman Tinubu da jam’iyyar APC ba tare da saninsa ba.

Tun da farko, masu shigar da kara sun kira shaidarsu ta 19 (PW19), Alex Ter, wanda ya shaida mahangarsu na farko da ya ba da shaida.

Ter dai lauya ne kuma dan siyasa, Ko’odinetan jam’iyyar PDP na kasa.

Abubakar Mahmoud, SAN lauyan INEC, ya nuna rashin amincewarsa a lokacin da shaidan ke shirin amincewa da furucin nasa wanda ya fi daya.

Mahmoud ya shaidawa Kotun cewa sun ki amincewa a ranar 20 ga watan Mayu kan amsar da masu shigar da kara suka bayar da karin bayanan.

Ya bayyana cewa ba a yi daidai da tanade-tanaden doka ba, don haka ya bukaci kotun da ta yi watsi da shi tare da tabbatar da hakan.

Sai dai ya shaida wa kotun cewa zai ajiye dalilansu na kin amincewa da a sanar da su a adireshin karshe

Lauyan masu shigar da kara ya shaida wa kotun cewa korafin da INEC ta gabatar an yi jayayya da hukuncin da kotun ta kebe.

Duk wani korafi da INEC ta yi a ajiye shi a gefe,” in ji Uche.

Don haka ya bukaci kotun da ta yi watsi da wannan korafin sannan ta kyale a ci gaba da aikin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *