Shugaban jam’iyyar APC Na Kasa, Ganduje Ya Kaiwa Rabiu Kwankwaso Farmakin Siyasa

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso ba’a kan rashin nada shi minista.

Alfijir Labarai ta rawaito Ganduje a wani faifan bidiyo a ranar Litinin ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya goyi bayan rugujewar gine-gine da aka yi a Kano.

Ganduje ya yi magana da wasu magoya bayansa da magoya bayan jam’iyyar na jihar Kano da suka kai ziyarar ban girma a sakatariyar.

A cikin faifan bidiyo mai tsawon mintuna biyu da dakika 28, Ganduje ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu yana da wayo don ganin yadda Kwankwaso ke son zama Ministan Babban Birnin Tarayya.

Ya kara da cewa rusa gine-ginen da gwamnatinsa ta amince da shi, ita ce hanya daya tilo da shi da Gwamnan Kano, Abba Yusuf za su iya bayyana bacin ransu a karkashin fakewa da tsaftace tsarin Kano.

“Shin ba mukamin ministan babban birnin tarayya ya ke so ba, shi ya sa ya ruguza gine-gine a Kano da sunan cewa yana son ya kare tsarin mulki.

Idan ka tambaye shi menene babban shirin, ba zai iya gaya maka ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *