Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Ash-Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau , ya yi kira ga daukacin limamai da al’ummar Musulmi a faɗin Najeriya da su tsayar da addu’o’in qanuti a cikin sallolinsu, sakamakon ta’azzarar rikice-rikice a Gabas ta Tsakiya da kuma ƙarin hare-haren ta’addanci da ake fuskanta a cikin ƙasar nan.
Sheikh Bala Lau ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 3 ga Maris, 2026, yayin Tafsirin Ramadan da yake gabatarwa a Yola, Jihar Adamawa. A cikin jawabin nasa, ya nuna alhini matuƙa kan yadda ake ci gaba da salwantar da rayukan jama’a, inda ya ce mafi yawan waɗanda abin ya shafa Musulmi ne marasa laifi.
“Abu ne mai tayar da hankali yadda rayuka ke salwanta ba gaira ba dalili,” in ji shi. “Iyaye, mata da yara suna shiga cikin halin ƙunci da rarrabuwar kawuna sakamakon rikice-rikicen da ke ƙara tsananta.”
Malamin ya bayyana cewa halin da ake ciki babbar jarabawa ce ga al’ummar Musulmi da ma duniya baki ɗaya, musamman idan aka yi la’akari da cewa tashe-tashen hankulan na faruwa ne a yankunan da ke da muhimmanci a tarihin Musulunci.
Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda hare-haren ta’addanci ke ƙara ƙamari a wasu sassan Najeriya, inda ya ce al’ummomi da dama na rayuwa cikin fargaba sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
“Ba za mu manta da abin da ke faruwa a ƙasarmu ba,” in ji shi. “’Yan ta’adda na ci gaba da ƙara kai hare-hare, al’ummomi na fuskantar barazana, kuma zaman lafiya na ƙara shiga hatsari. Wannan na buƙatar mu tashi tsaye da addu’a da kuma gyaran halaye.”
Sheikh Bala Lau ya buƙaci limamai su ware lokaci a cikin salloli domin yin qunut, tare da roƙon Allah Ya kawo ƙarshen zubar da jini, Ya kare bayinSa,Ya ba shugabanni hikima, tare da dawo da zaman lafiya a duniya da Najeriya baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa watan Ramadan wata dama ce ta tuba, komawa ga Allah, da kuma neman rahama a lokutan ƙalubale.
A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya kawo sauƙi ga waɗanda ke cikin ƙunci, Ya kawo ƙarshen rikice-rikice, kuma Ya wanzar da zaman lafiya mai ɗorewa a duniya da ƙasarmu Najeriya.
“Allah Shi ne Mai iko a kan komai,” in ji shi. “Gare Shi muka dogara, kuma gare Shi muke roƙon mafita da zaman lafiya.”
Jibwis Nigeria
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t