Shugaban Kamfanin ATM HOMES & Apartment Ya Gwangwaje makarantar KADA Da Makudan Kuɗaɗe

IMG 135228 31825 1756644760336

Mustapha Salisu.

Shugaban Rukunin Kamfanin ATM HOMES & Apartment, Arc. Dr Saleem Ahmad Ya gwangwaje makarantar KADA da kyautar Naira miliyan daya, Sannan ya jaddada Kudirin sa na cigaba da Tallafawa al’umma da kudi da kuma daukan nauyin karatun Dalibai.

Arc. Ahmad ya bayyana hakane yayin gangamin zagayowar Ranar Cigaban Al’ummar Kanam na Shekarar 2025 da kuma bikin yaye Dalibai karo na 4 na Makarantar KADA Special Academy da ya gudana a dakin taro na Dengi, Karamar Hukumar Kanam.

Dr Ahmad wanda yake matsayin Babban Jami’in tattara kudi na Kungiyar cigaban al’ummar Kanam, (KADA) ya bayyana Kudirin sa na daukar nauyin Dalibai 5 a katafariyar Makarantarsa ta ATM Real Estate Academy Dake Kano tare da horas da Dalibai mata 20.

Dr Wanda ya sami wakilcin Babban Jami’in gudanarwa na Kamfanin Abdurrasheed Ghambazai, yayi bayanin cewa wannan tallafi na daga cikin manyan kudirorin Shugaban Rukunin Kamfanin na tallafawa jama’a da kuma baiwa dalibai damar karo karatu da gurabe na samun horon sanaoi.

Idan Za a iya tunawa, Shugaban kamfanin, bayan kai ziyartar wata Makaranta a kano yayin bikin yaye Dalibai 100, ya gabatar da makamancin wannan kokari na daukar nauyin horas da dukkan Daliban da makarantar ta yaye.

“Tabbas wannan gudunmawa da yake bayarwa, magana ta gaskiya, ya jima yana gabatar da hakan ga dandazon al’umma” Acewar wani mazaunin yankin

Abdurrasheed daga nan ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafawa cigaban wannan kungiya ta KADA don samun kammala manyan azuzuwa 3,  da dakunan gwaje gwajen kimiyya da Gidauniyar ta assasa don cigaban mutanen Kanam da kewaye.

Shugabannin al’umma, masu rike da masarautun gargajiya da Dalibai sun yaba da kokarin Dr Saleem Ahmad a matsayin sa na wani ginshikin tallafawa cigaban ilimi da ayyukan cigaba da al’umma baki daya.

A yayin Gangamin, Barista Muntasir Adamu Kanam Ya Gabatar da makala mai taken “Cigaban Karamar Hukumar Kanam, Don  Cimma Muradan Karni Na Shekaru 25:

A yayin makalar, Gidauniyar cigaban Kanam da kewaye sun yabawa wasu mutane guda 6, bisa ga irin tsayin daka da jajircewa da suke bayar wa wajan cigaban yankunan afannonin rayuwa daban daban.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *