Shugaban Kasuwar Singa Ta Kano Ya Bayyana Abu Guda da Zai Sa Farashin Kayan Ya Sauka

Screenshot 20240417 090022 Facebook

Shugaban gamayyar kungiyoyin kasuwar Singa dake jihar kano, Batista Junaidu Muhammad Zakari yayi kira ga Kamfanonin da suke Samar da kayayyakin masurufi, da su ji tsoron Allah wajen ragewa al’umma farashin kayayyakin sakamakon saukar da farashin Dala ke yi a kowacce rana.

Alfijir Labarai ta ruwaito shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi wakilin Kadaura24 a Kano.

Yace ya Kamata a ce kayan masarufi Sun Fara saukowa, amma masu kamfanonin sun ki saukar da farashin nasu, wanda hakan tasa al’umma suke zargin mune mukaki sauka da farashin kayan duk kuwa da karyewar farashin dala.

Janaidu ya bayyana cewa, kungiyar a shirye take a kodayaushe wajen ci gaba da marawa Gwamnatin jihar Kano baya, domin inganta jin dadi da walwalar jama’ar jihar Kano.

Ya Kamata Gwamnati ta Fara Tilastawa Yan Kasuwa Don su Sauke Farashin Kayan su. Ya bukaci kungiyoyin da sauran al’ ummar Kasuwar ta Singa da su kasance masu baiwa Kwamatin tsaftar Muhallin da Ma’aikatan da za su yi aikin cikakken hadin domin ciyar da kasuwar da Kasuwanci gaba a fadin kasar nan..

Kadaura24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *