Shugaban kungiyar Amintattun Juna Yayi kira Ga Masu Kuɗi Suyi Koyi Da Halayen Marigayi Aminu Dantata Ko Sa Samii Kyakkyawan Shaida A Karshen Rayuwa

IMG 202527 29625 1751225154230

Shugaban kungiyar Amintattun Juna Aminu Umar Ɗan Sani Yayi kira Ga Masu Kuɗi Da Suyi Koyi Da Halayen Marigayi Alh Aminu Dantata na jin kan al’umma da kyautatawa ko wane bangare ko a samu Kyakkyawan shaida a Karshen rayuwarsu

Ɗan Sani ya bayyana alhininsa da sauran shuwagabannin kungiyar da lambobin na rasuwar hamshakin dan kasuwar nan mai aiyukan alheri, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Ya kuma bayyana rashin nasa a matsayin babban rashi ga kasa, la’akari da irin gudummawar da ya bayar wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya da ci gaban kasa baki daya.

Ya kara da cewa aiyukan alherinsa sun shafi rayuwar jama’a, musamman a bangaren ilimi da kiwon lafiya, gina matsa da sauran al’amuran ciyar da kasa gaba.

A ƙarshe ya mika sakon ta’aziyar kungiyar Amintattun Juna dake jihar Kano ga iyalan Alh Aminu Dantata, Gwamnatin Kano da daukacin al’ummar jihar, bisa wannan babban rashi na dan kasa mai daraja da zumunci da aka yi.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *