Daga Aminu Bala Madobi
Jarumar fina-finan Kannywood Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa duk da tana jin daɗin hulɗa da jarirái da yara kanana kuma suna bata sha’awa, to amma ba ta tunanin ta shirya háihuwar ƴaƴa na kanta, saboda ba zata iya daukar nauyi da ƙalubalen da ke tattare da renon su ba.
Alfijir labarai ta ruwaito fitacciyar jarumar ta wallafa hakan ne a shafinta na X, Nafisat ta nuna cewa “Ina son jarirai, ina son wasa da su kuma suna bani sha’awa to amma ba ni da juriya wajen rigimarsu, idan yaro ya rikice maka da rigima wani lokacin sai ka rasa ina zaka saka kanka.
Don haka bana tunanin zan yarda na haifi jarirai na kaina…” a cewar Jarumar
Me zaku ce?
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj