Shugaban Najeriya Ya Soke Harajin Wasu Kayayyakin Da Ake Shiga Dasu Najeriya

FB IMG 1742320893164

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bawa hukumar hana fasa kwauri ta kasar (Customs), umarnin daina karbar Haraji kan wasu Kayayyakin da ake shiga da su kasar.

Babban Kwantirolan Hukumar na kasa, CG Bashir Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya ce Tinubu ya ɗauki matakin ne domin bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma samar da walwala a tsakanin jama’a.

A cewar Adeniyi, “Cire harajin kayayyakin zaifi shafar kayan da ake shigowa dasu Najeriya daga kasashen Afirka domin dacewa da yarjejeniyar cinikayya ta Nahiyar (African Continental Free Trade Agreement), baya ga ƙarfafa kasuwanci da kuma amfanar da damar kasuwanci mara haraji a tsakanin ƙasashenmu”.

Ya kara da cewa yarjejeniyar cinikayyar na nufin samar da kasuwar Afirka guda ɗaya ta kaya da aiyuka, inda ƙasashen Nahiyar za su rage haraji a hankali wanda ake fatan ya kai ga kayan da aka samar a Afirka sun sami damar shiga kasuwanni ba tare da biyan haraji ba.

A ƙarshe ya ce akwai abubuwan da za a kula da su a yayin aiwatar da yarjejeniyar kamar dokokin asalin kaya, rahotannin fifiko na kasuwanci, dakatar da haraji kan kayayyakin da ake musayar su a tsakanin ƙasashen da suka kasance a cikin yarjejeniyar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *