Shugabannin APC 37 Sun Jefa Kuri’ar Goyan Bayansu Ga Shugabancin Ganduje

Screenshot 20240418 143232 Facebook

Shugaban jam’iyyar APC 37 sun bayyana Goyon bayansu Ga Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ta hanyar jefa kuri’ar amincewa.

Alfijir Labarai ta ruwaito a ziyarar da Shugabannin jam’iyyar APC na kasa suka kai a sakatariyar jam’iyyar APC a Abuja jiya, sun bayyana amincewar su ga Ganduje ta hanyar jefa kuri’ar amincewa.

A nasa jawabin, Shugaban riko na Kungiyar Shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar, Kuma Shugaban jam’iyyar a jihar Legas, Cornelius Ojelabi, ya bayyana cewa waɗanda suka Dakatar da Ganduje ba ya’yan jam’iyyar Bane

Yace, “Mun zo nan ne domin mu sanar da ku cewa muna bayanku da gaske. Dakatar da ake zargin ba daga ‘ya’yan jam’iyyar ba ce, amma ta fito ne daga mutanen da ke son kawo cikas ga jam’iyyar.

“Mun zo nan ne domin mu nuna hadin kanmu da kuma sadaukar da kai don jin dadin abin da mambobin kwamitin ayyuka na kasa ke yi na tsayawa tare da ku ta hanyar ba ku cikakken goyon baya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *