Ta Leko! Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Shirin Baiwa Ɗalibai Bashi

Screenshot 20240302 001733 com.facebook.katana edit 3844162523371

Gwamnatin tarayya Najeriya ta dakatar da kaddamar da shirin bayar da lamuni na daliban Najeriya har sai baba tagani.

Alfijir labarai ta rawaito Akintunde Sawyer, Babban Sakatare na Asusun Ba da Lamuni na Ilimi na Najeriya (NELFUND) ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da ARISE NEWS.

An sake dage ƙaddamar da shirin na bada lamunin da aka tsara zai fara a ranar Alhamis, saboda akwai wasu gyare-gyare da ake yi domin kaddamarwar, a cewar Sawyer.

“Abin takaici, ba zan iya cewa takamaiman Sai yaushe ba. Muna jira don tabbatar da cewa duk masu ruwa da tsaki sun hada kai don tabbatar da cewa babu wanda ya aka mance, sannan za mu iya fitar da wannan ta hanya mai ma’ana, cikakkiya kuma mai dorewa.

Shugaba Bola Tinubu ne ya rattaba hannu kan kudirin dokar bada lamunin a watan Yunin 2023, don kafa Asusun Lamuni na Dalibai (SLF) da bayar da lamuni marar ruwa ga ɗalibai a ƙasar.

Kudurin, wanda Femi Gbajabiamila, tsohon kakakin majalisar wakilai ne ya dauki nauyinsa, an shurya shirin fara shi ne tsakanin Satumba da Oktoba 2023.

Shugaba Tinubu ya sanar da fara shirin ne a watan Janairun 2024, bayan da gwamnatinsa ta gaza cika wa’adin watan Oktoban bara.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *