An yi awon gaba buhunan shinkafa da kwalayen taliya da sauran kayan abinci daga motocin
Alfijir labarai ta rawaito jama’ar gari sun tare hanya suna tare motocin kayan abinci, suna daka musu wawa a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Alhamis
Wani ganau, Alhassan Abdullahi, ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan daban sun tare motoci da dama da suka dauko kayan abinci daga Abuja zuwa Kaduna a daidai Mahadar Suleja da ke kan hayar.
A cewarsa, mutanen sun wasushe buhunan kayan abinci, musamman shinkafa daga motocin kafin sojoji su kawo dauki.
“Sai dai sojoi suka so suka fara harbi a iska domin tarwatsa bata-garin, amma duk da haka mutane da dama a cikinsu sun yi awon gaba buhunan shinkafa da kwalayen taliya da sauran kayan abinci.
“Ga shi mun ji an ce gobe yan acaba za su yi zanga-zangan da suka shirya yi jiya, amma suka dage,” in ji shi.
Inda Ranka
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V