Ta Sake Faruwa! Rundunar Yan Sandan Kano Ta Sake kama Yan Fashi 4 da Mai Kera Musu Bindiga A Hanyar Gezawa.

Ta sake Faruwa! 
Rundunar Yan Sanda kano sun sake kama Yan fashi masu tare hanya Gezawa a kano da mai kera musu bindiga sunzo hannu

Best Seller Channel

Best seller Channel 
Best Seller channel ta rawaito kakakin Yan Sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yana bayani yayin holin Yan Fashi a ranar Lahadi, bayan kimanin kwana 34 da shigar da koradin da wani Mai babbar mota yayi bayan da suka suka musu fashin a hanyar Gezawa zuwa Warawa. 

Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi ya umurci jami’in ‘yan Sanda na “Operation Puff Adder”. Kan kace kwabo Karkashin Jagorancin DPO na Gezawa CSP Haruna Iliya cikin taimakon Allah aka samu Nasarar kama Yan Fashin su 4a ranar 18, ga Dec 2021, an Kuma kama su da Bingida guda 1 da man wayar wannan bawon Allah Mai babbar motar nan da ya shigar da korafi aka su. 

Kiyawa,ya Kara da cewa, bayan fadada bincike ne aka kamo wanda yake kera musu makaman da suke amfani dasu wajen tare hanya da fashi da makami. 

Ga yadda tattaunar tasu ta kasance cikin video. 

Best seller Channel 


Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, ya kara gargadin cewa, masu aikata laifuka ba za su samu mafaka a jihar Kano ba. 

Su shiryu ne ko dai su bar Jihar gaba daya, in ba haka ba, za a kama su kuma su fuskanci fushin Doka. 

Ya kuma godewa al’ummar Jihar Kano bisa addu’o’i da karfafa gwiwa da goyon baya da hadin kai. 

Best Seller Channel 

Kwamishinan ya kuma bukaci mazauna yankin da su yi wa Jiha da kasa addu’a tare da kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su kuma kada su dauki doka a hannunsu. Za a ci gaba da sintiri sosai da kai hare-hare na maboyar miyagu da bakar fata a fadin jihar, saboda rundunar za ta ci gaba da gudanar da aikin “Operation Puff Adder”.Sanarwar da ta fito ne ta bakin kakain rundunar Yan Sandan kano

DSP ABDULLAHI HARUNA KIYAWA

Slide Up
x