IGP ya mika rahoton Abba Kyari ga hukumar ‘yan Sanda. Kan zarginsa da laifin badakalar dala miliyan $1.1m ta intanet

 IGP ya mika rahoton Abba Kyari ga hukumar ‘yan Sanda. 

Best Seller Channel 

Best Seller Channel

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya mika rahoton kwamitin binciken da aka dakatar da shugaban kungiyar amsa bayanan sirri, Abba Kyari, ga hukumar ‘yan sanda. 

Hakan na zuwa ne kusan watanni shida bayan da SIP karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike ta mika rahoton ta ga IG. 

Wani kwamishina a hukumar ta PSC Austin Braimoh, ya tabbatarwa da wakilin jaridar the Punch a ranar Lahadin da ta gabata cewa hukumar za ta tattauna kan lamarin a wannan mako. 

Best Seller Channel 

Ya ce har yanzu kwamitin Da’a na PSC na ci gaba da gudanar da rahoton, inda ya kara da cewa za a gabatar da rahoton ga zauren majalisar. 

“Kwamitin dindindin na ci gaba da gudanar da rahoton bayan haka za su gabatar da shi ga zauren majalisar domin daukar mataki,” in ji shi a wayar tarho. 

“Wakilinmu ya ruwaito cewa an tambayi Kyari kuma an mika martaninsa ga kwamitin ladabtarwa na rundunar. 

An dai bincikar Kyari ne bisa zarginsa da laifin badakalar dala miliyan $1.1m ta intanet daga wani fitacce a Instagram, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi, da wasu mutane hudu. 

Binciken ya biyo bayan tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta yi wanda ya ba da shawarar a mika shi ga Amurka domin yi masa shari’a. 

Best Seller Channel 

Wani wakili na musamman a hukumar ta FBI, Andrew Innocenti, ya yi zargin cewa Hushpuppi ya kulla yarjejeniya da Kyari bayan wani “mai hada baki,” Chibuzo Vincent, ya yi barazanar fallasa zargin damfarar dala miliyan 1.1 da aka yi wa wani dan kasuwa dan kasar Qatar.

Slide Up
x