Ta’adanci! Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Abuja Sun kuma Sace Mutane da Dama

IMG 20240121 062815

Daga Aminu Bala Madobi

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindiga da yawansu ya zarce 40 sun kai sabon farmaki karamar hukumar Bwari da ke FCT, Abuja Sun kai farmakin ne gundumar Kawu, inda suka yi awon gaba da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na gundumar tare da yaransa hudu

Haka kuma sun yi awon gaba da amaryar mai gundumar garin tare da yaronsa Lukman, sun kuma sace sarkin pawa da matansa da yara

Alfijir labarai ta rawaito yan bindiga sun kai sabon farmaki gundumar Kawu da ke karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.

A yayin harin, sun yi awon gaba da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na gundumar, Alhaji Alhassan Sidi Kawu da ƴayansa hudu da wasu mutane 18.

Shugaban karamar hukumar Bwari, Abdulmumini Zakari, ya shaidawa manema labarai cewa ƴan bindigar sun dira gundumar ne a ranar Laraba daga dajin Kuyeri da ke Kaduna.

Ya kara da cewa akwai mata da yaron mai gundumar yankin, Alhaji Abdulrahman Danjuma Ali a cikin wadanda aka sace, rahoton The Punch. Yadda ƴan bindigar suka kai farmakin Zakari ya ce: “Sun raba kansu ne gida gida, wasu suka tafi gidan mai sarautar gudnumar, Alhaji Abdulrahman, inda suka sace amaryarsa da yaronsa Lukman.

“Wasu kuma sun farmaki gidan Alhaji Alhassan Sidi Kawu, Marafan Kawu kuma tsohon shugaban PDP na gundumar, sun tafi da shi da yaransa hudu.” Yan sanda ba su ce uffan kan harin ba Haka kuma an ruwaito cewa ƴan bindigar sun farmaki gidan Sarkin Pawan Kawu, Gambo Pawa, wanda suka sace shi tare da matansa biyu da yara.

Duk wani yunkuri na manema Labarai na jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ya ci tura.

News NG

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *