Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci gawar wani dan jarida na kamfanin sadarwa na Atar Communication, mamallakan gidan talabijin na Liberty TV/Radio a ranar Laraba a Abuja, kwanaki biyar bayan an bayyana bacewarsa.
Alfijir labarai ta ruwaito Ɗan jaridar, mai suna Joel Waksi, an ce ya bar ofis da misalin karfe 9 na daren ranar Juma’a kuma ana sa ran zai dawo bakin aiki da karfe 2 na rana a ofishin su da ke Mpape.
Babban Manajan Kamfanin, Balarabe Muhammad, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga City & Crime, ya ce rundunar ‘yan sandan reshen Mpape ta sanar da cewa an ga gawarsa kusa da yankin Panteka kuma an ajiye gawar a babban asibitin Kubwa
Ya ce an caka masa wuka a wuyansa, kuma wayarsa ta bata.
Ya ce, “An yi zargin cewa masu ƙwacen waya ne suka kai masa hari,” ya kara da cewa watanni biyu baya, ya tsallake rijiya da baya, inda aka caka masa wuka a karkashin cikinsa, amma aka yi masa magani ya warke,” in ji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj