Takaitaccen Tarihin Hijra A Musulunci Da Watannin Shekarar Musulunci

IMG 20231007 WA0127 edit 10731539781694

TAKAITACCEN TARIHIN HIJRA A MUSULUNCI

Farkon faruwar tarihin shekarar Musulunci (Hijra) wani abu ne mai fadi da kuma dogon tarihi.

Amma dai ta samu asalinta ne a lokacin Khalifancin Sayyidina Umar a sakamakon wani abu da ya afku a lokacinsa a cikin watan Sha’aban, wadda kuma aka yi kokarin tantance wane a Sha’aban ne, amma abin sai ya faskara.

Wannan ne ya sa Sayyidina Umar ya tara sahabbai,inda ya nemi shawarar yadda za a rika tantance tarihin faruwar al’amura a Musulunci.

Don haka sai shawara ta tsaya a kan fara lissafin kalandar Musulunci daga Hijrar Manzon Allah daga Makka zuwa Madina, aka kuma sanya watan Muharram ya zama shi ne watan farko a cikin jerin watannin Kalandar Musulunci.

WATANNIN SHEKARAR MUSULUNCI

An ruwaito cewa tun kafin zuwan Musulunci,daya daga cikin kakannin Annabi Muhammad (S.A. W) wanda ake kira Kilab bin Fihr shi ne wanda ya ayyana wa watannin goma shabiyu sunaye da ake kiran su da su.

Bayan zuwan Musulunci, kasancewar watanni sha biyu su ne a cikin Addinin sai ya kar6i wadannan sunaye ya ci gaba da ambaton watannin da su.

(I) AL-MUHARRAM

(2) SAFAR

(3) RABI’UL AWWAL

(4) RABI”UL AKHIR

(5) JUMADAL ULA

(6)JUMADA AKHIR

(7) RAJAB

(8) SHA’ABAN

(9)RAMADAN

(10) SHAWWAL

(II) DHUL-KIDA

(12) DHUL-HIJJAH

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *