Takaitaccen Tarihin Marigayi Farfesa Jibril Isa Diso Nakasa Ba Kasawa Ba

Screenshot 20240713 093912 Facebook

An haifi marigayi Farfesa Jibril Isa Diso a Unguwar Diso dake karamar hukumar Gwale a Jihar Kano a ranar 22 ga Watan Afirilun shekarar 1955.

Ya fara karantunsa na Furamare a shekarar 1962 inda ya gama a shekarar 1969.

Daga nan Farfesa Jibiril Isa Diso ya wuce Makarantar sakandire koyar da makafi ta Gindiri Blinds Secondary School dake Jihar Filato a shekarar 1979 .

Bayan marigayin Farfesa Diso ya kammala makarantar sakandire wanda tun Yana jariri ya kasance makaho, sai ya nemi shiga Jami’ar Bayaro dake Kano,saidai bayan ya samu gurbin shiga Jami’ar kuma rahotonni suka tabbatar dacewa babu sashen koyar da dalibai masu bukata ta musamman irinsa ,sai Jami’ar ta Bayaro ta bude sabon sashen koyar da dalibai masu bukata ta musamman a shekarar 1984 saboda Farfesa Jibiril Diso.

Daga nan, ya kasance Dalibi na farko da aka dauka kuma aka bude sashen koyar da dalibai masu wannan matsala saboda dashi.

A shekarar 1991, Farfesa Jibiril Isa Diso ya samu digirinsa na uku a Jami’ar Birmingham dake birnin London (PhD ) bayan kammala digirinsa na farko da na biyu a Jami’ar Bayaro.

Bayan kammala karantunsa na digiri na uku,ya fara koyarwa a makarantar Tudun Maliki a cikin birnin Kano a shekarar 1992 .

Sai kuma a shekarar 1994 ya koma Jami’ar Bayaro dake Kano inda ya koma koyarwa acan, kuma ya jagoranci sashen koyar da dalibai masu bukata ta musamman din.

A shekarar 2019 bayan yayi rubuce rubuce duk da Lalurar rashin ganinsa, Farfesa Jibiril Isa Diso ya zamo Farfesa na farko a Najeriya da ya rike Wannan matsayin a tahirin Najeriyar.

Kafin mutuwarsa ya rubuta litattafai guda 10 da har yanzu ake buga misali akansu .

Bayan zamowa Farfesa na farko, kuma makaho a Najeriya, ya karya duk wani tarihi da hasashen da ake cewa Nakasa kasawa ce a Najeriya dama Afrika.

Shine mutum na farko da ya yaki cin zarafin da ake yiwa masu bukata ta musamman, sannan lokacin da tsohon Gwamnan jihar kano Malam Ibrahim Shekarau ya nadashi a matsayin mai bashi shawara akan makafi da guragu da kutare, ya gargadi jama’a da a daina kiran Iran wadannan mutane da wannan suna, maimakon haka a koma Kiransu da sunan masu bukata ta musamman.

Kafin rasuwarsa a rana babba irin wannan wato Juma’a 12 ga wata Yulin 2024, ya yaye dalibai sama da 300 daga Jami’ar Bayaro kuma yawancinsu masu bukata ta musamman.

Ya gabatar da shirye shirye na karfafawa dalibai irinsa guiwa a gidajen Radio da Talabijin da Jaridu musamman Rahma Radio da Talabijin inda yake gabatar da shirin wani Zomo na tsawon wani lokaci.

Tuni Al’umma daga Sassa daban daban na Najeriya ke cigaba da nuna alhininsu na rashin da akayi a kano dama Najeriya baki daya.

Hajiya Binta Abdullahi Sarki Muktar,shugabar kafafen yada labarai na Rahma Radio da Talabijin ta nuna kaduwarta abisa rashin Farfesa Jibiril Isa Diso,inda tace dalibai a Najeriya da masu tasowa a bangaren ilimin Masu bukata ta musamman zasu jima suna kewarsa.

Wani babban abin jin dadi shine, kaf cikin Iyalansa babu mai bukata ta musamman.

Wanne darasi ya kamata ku koya musamman masu bukata ta musamman daga rayuwar Marigayi Ferfasa Jibril Isa Diso?

Rahama Radio

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *