Takaitattun Labaran Duniya a Safiyar Laraba 04/10/2023 19/03/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Majalisar Dattawa ta hana sabbin Sanatoci tsayawa takarar shugabancin majalisar.

Rundunar sojin Najeriya za ta yi bincike a kan zargin rashin ciyar da dakarunta da ke filin daga.

Hukumomin jami’ar Usmanu DanFodiyo da ke jihar Sokoto ta musanta cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a harabar jami’ar sunce kawai ‘yan fashi ne.

Kotun zaɓen ƴan majalisar dokokin jihar Abia ta kori ƙarar da ɗan taƙarar LP ya shigar kan ɗan majalisar PDP na Obingwa ta Gabas.

Rundunar ƴan sandan jihar Legas tace tana tsare da Naira Marley kan mutuwar tsohon abokin aikinsa Mobhad.

’Yan sanda sun kama mutum 14 da suka ce an sace musu mazakuta a Abuja.

Gwamnatin Kano ta ayyana yau Labara amatsayin hutu saboda Bikin Maulidi.

Wata kungiyar matasa a garin Potiskum na jihar Yobe ta gudanar da zanga-zangar lumana da tattaki kan yawaitar matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

An yanke wa soja hukuncin kisa bisa laifin kashe masu zanga-zanga a DR Kongo.

Ɗalibai 95 sun kamu da wata baƙuwar cuta a Kenya.

Ƴan sanda sun kama iyayen da suka yi wa yaransu auren wuri a Indiya.

Majalisar dokokin Armenia ta kada kuri’ar amincewa da shiga kotun ICC.

UCL: Galatasaray ta sami nasara akan Manchester United da ci 3:2 a wasan jiya.

UCL: Lens ta sami nasara akan Arsenal da ci 2:1 a wasan jiya.

UCL: Real Madrid ta sami nasara akan Napoli da ci 3:2 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *