Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Asabar 29/07/1445AH – 10/02/2024CE

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu zai tafi Abidjan na Kasar Côte d’Ivoire don mara wa tawagar ‘yan wasan Super Eagles baya.

’Yan sanda sun kama ’yan bindiga mata biyu tare da gungun wani jagoran ’yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Abuja.

Gwamnan Katsina Dikko Radda yace ’yan bindigar da jami’an tsaro suka hana sakat a jihar na ci gaba da kokarin kawo masa hari, sai dai hakan ba zai sa ya ɗaga kafa a kokarin sa na kakkabe su daga jihar domin tabbatar da zaman lafiya ba.

EFCC ta ayyana neman uwargidan Godwin Emefile ruwa a jallo.

An gudanar da zangar-zanga kan matsin rayuwa da rashin tsaro a Osun.

An yi garkuwa da mutane 16 da suka hada da yara da mata a kauyen Kogo da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Matatar mai ta Dangote za ta fara sayar da man fetur a Najeriya, a cikin makonni masu zuwa.

Wani direban motar bas ya cinnawa wani jami’in hukumar mai kula da zirga-zirgan ababen hawa a jihar Edo wuta sannan ya tsere.

Dangote ya alƙawarta tallafa wa tsare tsaren taimaka wa al’umma da ci gabansu don magance matsalolin tattalin arziki a jihar Kano yayi wnnan alƙawarin ne a lokacin da ziyarci gwamnan jihar Kano Abba Yusuf.

Kungiyar ‘Yan Kasuwa a Jihar Yobe, sun gudanar da sallah da addu’ar neman samun sauki kan kan tsananin rayuwa da ake fuskanta a Najeriya.

Tarzomar adawa da dage zabe ta sake ballewa a Senegal.

Manyan jam’iyyun adawa a Pakistan sun yi ikirarin samun nasara a babban zaben kasar.

Gwamnatin Madagascar ta kare kudurin dandaƙe masu fyaɗe.

Jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Senegal.

Laliga: Real Betis ta sami nasara akan Cadiz da ci 2:0 a wasan jiya.

Bundesliga: Dortmund ta sami nasara akan Freiburg da ci 3:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *