Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Talata 03/08/1445AH – 13/02/2024CE

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Hukumar HISBA a Kano ta kama shararriyar mai amfani da TikTok ɗin nan, wato Murja Ibrahim Kunya bisa zargin aikata badala da abubuwan da ba su dace ba a shafin sada zumunta.

Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutum biyu (mace da namiji) kan yin sharholi ta kwanciya a cikin cocin ADC a kwalejin ‘yan sanda a Maiduguri.

NDLEA ta samu wata mai ciki, Amarachi Akaolisa tana harkar saida kwayyin Oraifite da Umuni Evili a jihar Anambra.

Wasu tsagerun ƴan bindiga sun halaka jami’in ɗan sanda ɗaya tare da kwance fursunoni bakwai yayin da suka kai hari agidan gyaran halin Okigwe dake jihar Imo.

Gwamnonin PDP sun buƙaci a kafa ƴansandan jihohi.

Hukumar DSS ta cafke Sunusi Oscar 44 na masana’antar Kannywood, bisa furta kalaman barazanar kisa

Sheikh Auwal Sharrif Zaria ya amsa tambayoyi a ofishin hukumar DSS a Kaduna ana zargin malamin da kwatanta mulkin Buhari da Tinubu kamar na Fir’auna da Hamana.

EU tace ya kamata kasashen kawance su daina taimakawa Isra’ila da makamai.

Afirka ta Kudu za ta tura dakaru 2,900 don yaƙi da ƴan bindiga a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

Ahmed Musa ya buƙaci a daina aibata Alex Iwobi.

EPL: Chelsea ta sami nasara akan Crystal Palace da ci 3:1 a wasan jiya.

Seria A: Udinese ta sami nasara akan Juventus da ci 1:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

Takaitattun labarai https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *