Yadda Nisabin Zakka Da Sadaki Da Diyyar Rai, Yake Kaiwa Da Komowa A Shekarar, 1445 AH 2023/24

FB IMG 1707823520507

Yadda take kasance a shekarar musulunci ta 1445 AH wajen fitar da hakkin Allah na zakka, sadaki, diyyar Rai a wannan lokacin.

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar Shari ah ta jihar Kano ta wallafa yadda nusabin zakka, sadaki da diyyar rai yake ta bana shekarar 1445 Ah 2023, kamar yadda ta saba duk shekara.

Sai dai duba da yanayin tashin kudaden ketare da ke faruwa Sheakh Ibrahim Falaki ya sabunta yadda nusabin yake a wannan lokacin.

      MAFI KARANCIN SADAKI

₦50, 008. shine mafi karanci a baya kafin Kara tashin Gauron Zabi da kudaden suke yi.

Amma a yanzu SADAKI ya koma: ₦79,687:00,
amma mutum zai iya bada sama da haka bisa kyautatawarsa.

Amma a cewar Malam Ibrahim Khalil sadaki har yanzu Yana Nan a dubu Ashirin 20,000.

   Kimar Yanke Hannu A Sata

₦50,008 shi ne kimar da za a yanke hannu a idan mutum yayi sata.

NISABIN ZAKKA

A baya Yana farawa ne daga ₦4000,695,00

Amma a yanzu Yana farawa ne daga: ₦6,375,000:00

Za a kasa wannan kudin gida (40) wanda zai zamanto ₦157,390,00 shi za a bayar

Idan kudin ya kai Miliyoyi, kowace Miliyan Ɗaya za a fitar mata da ₦…..

Kuɗin Azurfa, Nisabin zakkarsu zai kama, ₦341,946,5, abin da za a fitar shine ₦8,543,66.

DIYYAR RAI A MUSULUNCI :

A baya farkon shekarar ₦200,034,750,00.

A yanzu tsakiyar shekarar ₦318,750,000:00

Wannan kimar nisabin zai iya sauyawa daga lokaci zuwa lokaci,Sakamakon hawa da saukar Dinare da Azurfa.

NISABIN ZAKKAR DABBOBI
RAKUMA

RAKUMA: Daga (5 – 9) Akuya 1

Daga (10 – 14) Awaki 2.

Daga (15 – 19) Awaki 3

Daga (20 – 24) Awaki 4.

Daga (25) abin da yai sama za a fitar daga Rakuma.

SHANU: Daga (30) za a ba da Maraki

AWAKI/TUMAKI: Daga (40-120) za a ba da Akuya/Tunkiya.

Idan suka kai dari da ashirin da daya sai a ba da biyu har Zuwa dari biyu da daya, sai a ba da uku, daga nan kowace dari za a ba da ɗaya.

NISABIN ZAKKAR AMFANIN GONA

Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa goma (1/10) na noman ruwan sama, kwano (30).

Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa ashirin (1/20) na noman rani, kwano (15).

Wannan shine yadda zata kasance a wannan shekara ta 1445AH

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *