Daga Baba Usman Gama
Adadin wadanda suka mutu a jihar Filato ya karu zuwa 113, in ji wani jami’i, a yankin da ake yawan samun rikici tsakanin makiyaya da manoma.
An yi jana’izar mutum takwas da Æ´an bindiga suka kashe a Katsina.
‘Yan bindiga a jihar Taraba sun yi awon gaba da tsohon ciyaman na karamar hukumar Yorro, Hon. Ishaya Dimas Dila tare da wasu mutum 10 a kauyen Dila da Kunini.
Alamu sun nuna Austin Umahi zai iya zama magajin Sanata David Umahi a majalisar dattawa a Ebonyi
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatin tarayya karkashin jagorancin jam’iyyarsa za ta shawo kan kalubalen da kasa ke fuskanta.
Kungiyar Shi’a ta halarci bikin Kirsimeti a bana ma a jihar Kaduna kungiyar ta ziyarci cocin St. Joseph da ke Samaru a Zaria da ke jihar Kaduna.
Jihar Sokoto – Fitaccen Fasto, Mathew Hassan Kukah ya gargadi Shugaba Tinubu kan irin mulkin da ya ke yi a kasar.
Hamas da ƙungiyar Islamic Jihad sun ki amincewa da yarjejeniyar tsagaita yaki a Gaza.
Shugaban kasar Iran ya ce tabbas Isra’ila za ta gane kuranta na kashe babban kwamandan dakarun kare juyin juya hali na Iran a Syria.
Ma’aikatar Kudi ta Isra’ila ta ce yaÆ™in da Æ™asar ke yi a Gaza zai iya lashe Æ™arin dala biliyan 14 a shekarar 2024, adadin da ya ninka giÉ“in kasafin kuÉ—inta kusan sau uku.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp